Obama ya caccaki manufofin Trump
November 2, 2025
Tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya caccaki Donald Trump kan manufofinsa tare kuma da yin gargadi kan hadarin da ke barazana ga dimokuradiyyar Amurka, yayin da yake yi wa jam'iyyar Democrat yakin neman zaben yankunan da ake kallo a matsayin gwaji.
A lokacin da yake jawabi a wani birni da ke gabashin Virginia, mista Obama ya dasa ayar tambaya kan shin ko al'amura sun fara daidaita a Amurka watanni tara bayan hawan Trump kan madafun iko, sannan kuma ya caccaki manufofin tattalin arziki na shugaban da ya ce ba sa gyara kowa face shi kadai da iyalansa.
Mista Obama ya kuma soki 'yan jam'iyyar Republican wadanda a cewarsa ba sa iya takawa Trump birki duk da wuce gona da iri da yake yi, tare kuma da nuna damuwa kan yadda kotun kolin Amurka da ba ta nuna alamun dakatar da gwamnatin Trump kan amfani da take yi da karfin iko.