Rasha ta sake kai farmaki kan Ukraine
November 29, 2025
Harin an kai shi ne da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, inda suka lalata wasu gidaje da gine-gine a gundumomi daban-daban. A baya-bayan nan birnin Kiev na yawan fuskantar hare-haren jiragen sama na yakin Rasha mafiya muni wanda ke shafar tashoshin makashin kasar.
Ukraine na kare kanta daga mamayar da kasar Rasha ta fara tun a watan Fabrairun 2022, tare da gagarumin tallafi daga kasahen Yamma. Sai dai sabon farmakin ya zo ne yayin da ake sa ran tawagar Amurka za ta je birnin Moscow domin tattaunawa da Vladimir Putin kan shirin kawo karshen yakin wanda Shugaba Donald Trump ya gabatar mai dauke da shawarwari 28.
Daftarin shawarwarin guda 28, ana ganin ya ba wa Rasha fifiko ciki har da neman Ukraine ta hakura da wasu yankuna da Rasha ta kwace da rage yawan sojoji da janye batun shiga kungiyar tsaro ta NATO.
Shugabannin Turai na gaba gaba don ganin an cimma yarjejeniyar, bayan nuna fargabar makomar tsaron yakina nuna fargabar cewa yankunansu na cikin barazanar tsaro daga Rasha a nan gaba.