1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Shugaban Colombia ya kori jami'an diflomasiyyar Isra'ila

October 2, 2025

Shugaba Gustavo Petro ya kuma soke yarjejeniyar kasuwanci mara shinge da kasashen biyu suka rattabawa hannu a 2020.

https://p.dw.com/p/51Nvn
Shugaban kasar Colombia Gustavo Petro
Shugaban kasar Colombia Gustavo Petro Hoto: John Angelillo/UPI Photo/newscom/picture alliance

Shugaban Colombia Gustavo Petro ya sanar da cewa ya sallami dukkan jami'an diflomasiyyar Isra'ila da suka rage a kasar, bayan sojojin ruwan Isra'ila sun tsare jirgin flotila mai dauke da kayan agajin jinkai zuwa Gaza.

Karin bayani:Zaben shugaban kasa a Kwalambiya

Shugaba Petro ya ce daga cikin 'yan gwagwarmayar da ke cikin jiragen ruwan akwai wasu mata guda biyu masu rajin kare hakkin bil Adama 'yan kasar ta Colombia, wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin al'ummar Falasdinawa.

Karin bayani:Kotu ta yanke wa tsohon shugaban Colombia hukuncin daurin shekaru 12

A baya bayan nan shugaban kasar Colombia ya shiga sahun masu zanga-zangar adawa da yakin Gaza a birnin New York na Amurka, inda ya yi kira ga sojojin Amurka da su bijirewa Trump. Matakin da ya sanya hukumomin Washington DC soke bizar Mr. Petro.

The Global Sumud Flotilla wani rukuni ne na jiragen ruwa makare da kayan agajin jinkai wanda kuma ke dauke da fitattun 'yan gwagwarmaya daga kasashe daban-daban ciki har da 'yar fafutukar kare muhalli ta Sweden Greta Thunberg.