1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaUkraine

Chechnya: Zelensky ya ce Amurka ta kori Kadyrov

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 7, 2026

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bukaci Amurka ta kara yin matsin lamba ga Rasha, ta hanyar cire shugaban Chechnya Ramzan Kadyrov daga madafun iko

https://p.dw.com/p/56TrN
Ukraine | Volodymyr Zelensky | Amurka | Donald Trump | Kora | Chechnya | Shugaban Kasa | Ramzan Kadyrov
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr ZelenskyHoto: Joe Raedle/AFP/Getty Images

Volodymyr Zelensky ya yi wannan kiran ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, inda ya ce matakin cire Nicolas Maduro daga madafun iko a Venezuela ya nuna irin karfin da Washington ke da shi na tilasta Moscow, idan har ta yi niyya. Ya jaddada cewa korar Chechnya Ramzan Kadyrov zai sanya Shugaba Vladimir Putin na Rasha, sake yin tunani kan hare-haren da ya ke kai wa Ukraine. Kadyrov da ya kwashe shekaru biyu yana mulkin kama-karya a Chechnya, kuma ya sha nuna goyon bayansa da mamayar Moscow a makwabciyarta Ukraine, har ma da ba ta shawarar kai hari da makamin nukiliya.