1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Zelensky na shirin sake ganawa da Trump a Florida

December 28, 2025

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky zai gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a Florida a kokarin cimma matsaya kan daftarin tsarin zaman lafiya da zai kawo karshen yakin kasarsa da Rasha.

https://p.dw.com/p/562hn
Shugaba Zelensky na Ukraine da takwaransa Trump na Amurka
Shugaba Zelensky na Ukraine da takwaransa Trump na AmurkaHoto: Julia Demaree Nikhinson/AP Photo/picture alliance

Gabanin isar Zelensky Amurka tare da sabbin shawarwaru game da batu mai sarkakakiya kan kasarsa da ke hannun Rasha, shugaba Trump ya ce ba bu wani kari ko ragi da Kiev za ta yi a cikin daftanin muddin ba da izininsa ba. 

Daga nasa bangare ministan harkokin wajen Rasha Sergueï Lavrov ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na TASS cewa: Moscow za ta ci gaba da ba da hadin kai ga masu shiga tsakani na Amurka domin samar da dawamammar yarjejeniya da za ta magance rikicin tun daga tushe, kafin daga bisani ya soki kasashen Turai.

A jajibirin wannan ganawa ta Trump da Zelensky Rasha ta kaddamar ga gagarumin hari da jirage maras matuka da kuma makamai masu linzali a birnin Kiev fadar gwamnatin Ukraine, lamarin da ya yi ajalin mutane biyu tare da haddasa katsewar lantarki ga mutane sama da miliyan daya.