Martanin yunkurin juyin mulkin Jamhuriyar Benin
December 12, 2025
Tun dai wannan batu na juyin mulki da bai yi nasara ba na kasar Benin, da abubuwan da suka wakana a cikin sa na yada labarai marassa tushe daga bangarori da dama tare da ma da zarge-zarge marassa tushe da ‘yan shafukan sada zumunta ke yi kan wannan ko waccan kasa, wanda ga masana irinsu Dokta Atto Namaiwa Malami a jami'ar birnin Tahoua makomar huldar kasashen AES musamman ma Nijar da makwabtansu Jamhuriyar Benin da Najeriya zai danganta ne da binciken da kowa zai yi na ganin irin hannun da yake da shi ko cikin yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin ko kuma yunkurin saka rudani ga kasashen na AES ta hanyar kutse na jirgin sojan Najeriya.
Matsalolin da ake ciki
Sai dai masu lura vda al'amuran yau da kullum musamman a tsakanin wadannan kasashe makwabta juna irinsu Alhaji Oumaropu Dan Madamin Damagaram, suna ganin ECOWAS na kare martabar Dimukuradiyya ne a yankin wanda ya ce su dai fatansu shi ne na a samu zaman lafiya don bunkasar shige da fice tsakanin kasashen.
Wani fanni kuma da masna masu sharhi suka yi nazari a kanshi kann makomar hulda tsakanin kasashen na AES da Kasashe itrin su Benin da Najeriya, a fuskar Diflomasiyya ne kawai suke ganin raunin da za a iya samu ba wai a fannin hulda ta kasuwanci ko zamantakewa tsakanin al'umma ba.
Abun jira a gani dai shi ne yadda wadannan kasashe za su tunkari juna ganin babban matsalar a nan ita ce ta gurbacewar hulda tsakanin Faransa da kasashen AES, yayin da a hannu daya kasashe irinsu Jamhuriyar Benin da Najeriya da ke makwabtaka da AES ta fannin Jamhuriyar Nijar suke kara karfafa huldarsu da kasar Faransa.