Amurka da Rasha za su sake tattauna batun yakin Ukraine
December 18, 2025
Wakilan Amurka da Rasha za su gana da juna a birnin Miami na jihar Florida a karshen mako mai zuwa, domin nazartar shawarwarin shugaba Donald Trump, na kawo karshen yakin Ukraine, kamar yadda fadar White House ta sanar.
Wannan na zuwa bayan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya nuna gamsuwa kan yadda tattaunawarsa da wakilan Amurka a birnin Berlin na nan Jamus ta wakana a kwanan nan, inda ya yi gargadin cewa Rasha na shirin fadada yakinta a sabuwar shekara mai kamawa.
Karin bayani: Amurka ta ce Rasha na da niyyar katse yakin Ukraine
To sai dai fadar ta White House ba ta bayyana sunayen wakilanta da na Rasha da za su gana da juna ba.
A ranar Laraba aka jiyo shugaba Vladimir Putin na Rasha na ikirarin cewa tabbas Moscow za ta cimma dukkan kudorinta na wannan yaki, ciki har da kwace yankunan da ta ce mallakinta ne.