1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Shawarar Trump ce mafita ga Gaza?

Mahmud Yaya Azare LMJ
September 24, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump, na ci gaba da ganawa da shugabanin Kasashen Larabawa da na Musulmi a birnin New York, kan sabon kudiri da ya gabatar da zai kawo karshen yakin Gaza.

https://p.dw.com/p/511zg
Amurka | New York 2025 | Donald Trump | Ganawa | Kasashe | Larabawa | Musulmi | Gaza | Hamas | Isra'ila | Yaki
Shugaban Amurka Donald TrumpHoto: John Angelillo/UPI Photo/IMAGO

Ganawar tasu na zuwa ne, a daidai lokacin da ake taron Majalisar Dinkin Duniya zagaye na 80 ake kuma samun karin kasashen duniya da suke amincewa da kafuwar kasar Falasdinu mai cikakken 'yanci.

Wacce rawa wadanna kasashe za su taka a Gaza?

Shugaban Amurka Donald Trump dai ya gana da manyan Kasashen Larabawa da na Musulmin duniya bakwai da suka hadar da Saudiyya da Masar da Katar da Jordan da Turkiyya da Pakistan da kuma Indonosiya.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Yayin ganawar tasu Trump ya ce: "Dole ne mu kawo karshen yaki a Gaza a kuma saki ilahirin wadanda ake tsare da su......."

Matsin lamba da ga Hamas da kwace iko daga hannunta

Daftarin kudirin ya nemi kasashen su matsawa Hamas lamba ta sako wadanda take tsare da su nan take, kana kasashen su kafa rundunar tsaro da za ta maye gurbin dakarun Isra'ila da za su fice daga ilahirin Zirin na Gaza.

Ya kuma dorawa Kasashen na Larabadawa da na Musulmi alhakin sake gina Gaza, kana su kafa gwamnatin Falalsdinawa da ba za ta kunshi kungiyar Hamas ba.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani