1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Ana shirin zaben sabon magajin garin birnin New York

November 4, 2025

Ana sa ran fitar masu kada kuri'a sama da miliyan biyar domin zaben sabon magajin garin birnin New York na 111, inda hasashe ke nuna yiwuwar zabar matashi Zohran Mamdani mai shekaru 34 a duniya.

https://p.dw.com/p/532Jh
Runfar zabe a birnin New York na Amurka
Runfar zabe a birnin New York na AmurkaHoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

Al'ummar birnin New York na Amurka na zaben sabon magajin garin a wannan rana ta Talata, inda hasashen gabanin zaben ya nuna Zohran Mamdani, Musulmi mai shekaru 34 dan asalin kasar Indiya wanda ya fito daga jam'iyyar Democrat kuma mai tsananin adawa da manufofin Donald Trump a kan gaba.

Karin bayani: Obama ya yi kakkausar suka ga manufofin Trump

Za a bude runfunan zaben da kimanin karfe shida agogon Amurka wato karfe 11 agogon GMT, kana kuma a rufe su da kimanin karfe tara agogon Amurkar wato karfe biyu na daren ranar Laraba agogon GMT.

Masana kan harkokin zaben Amurka ciki har da farfesa Lincoln Mitchell na jami'ar Colombia na tsammanin fitowar jama'a masu yawa a wannan zabe da hamayya ke da matukar zafi.

Ana sa ran zaben na magajin garin birnin New York na 111 wanda zai fara aiki a ranar daya ga watan Janairu na shekara 2026 zai samu halatar masu kada kuri'a sama da miliyan biyar a birnin mafi girma a Amurka, inda jam'iyyar adawa ta Democrat ke da kashi 60% na al'umma masu goyon bayanta.