Rasha za ta mayar da martani mai zafi kan EU
December 5, 2025
Rasha ta yi gargadin cewa idan har Tarayyar Turai ta dauki kadarorinta ta taimaka wa Ukraine to ba shakka za ta mayar da martani mai zafi.
Wani Jakadan Rasha ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP hakan a yau Juma'a a matsayin martani ga yunkurin na EU.
Merz ya bukaci amfani da dukiyar Rasha a tallafa wa Ukraine
Shugaban Gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya bukaci gwamnatin Belgium ta amince a yi amfani da kudaden Rasha da aka toshe don tallafa wa Ukraine.
An shafe kusan shekara hudu ana gwabza fada tsakanin Rasha da Ukraine ba tare da cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba.
Amurka ta ce Rasha na da niyyar katse yakin Ukraine
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin dakatar da yakin na Rasha da Ukraine amma har yanzu ba a kai ga hakan ba tukunna.