Ina aka kwana kan batun kawo karshen yakin Iran?
May 26, 2026
Bayan kyakkywar fatar da akai tayi ta karatowar rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yakin Iran da Amurka,murna ta koma ciki, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya danganta yin hakan da wajibcin manyan kasashen Larabawa da na Musulman duniya.
Kasashen da suka hada da Sauidiya da Katar da Turkiya da Masar da Jodan da Pakistan da ma ita kanta kasar ta Iran, da koyaushe takenta shi ne, Allah rusa Isra'ila da Amurka, ya neme su da cewa babu makawa sai sun kulla hulda da Isra'ila karkashin wata yarjejeniya da ake kira Yarjejeniyar Abarham,in bah aka ba kuwa,to babu batun cimma wata yarjejeniya.
Sarkakiyar yarjejeniyar
Bugu da kari Trump ya sake lashe amansa dangane da batun mika makmashin nukiliyar Iran zuwa ga wata kasar ta daban, bayan da Iran ta amince da kasar China a matsayin wadda za ta dankawa, Trump ya dawo ya ce, dole ne a lalata shi.
Wannan matakin dagula lissafi a cewar masharhanta bai rasa nasaba ga irin sukar da Trump ke fuskanta daga kasarsa da ma daga Isra'ila kan cewa, za su tashi a tutar babu idan har yarjejeniyar da Iran ta karkare kan sabuwar fahimtar junar da za ta kai ga dagewa Iran takunkumi da dawo mata da makudan kudadenta da aka hanata taba su a bankunan kasashen duniya.
Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta sanar da cewa, babu wata alaka tsakanin sanya bakin da ta yi don gamsar da bangarorin Amurka da Iran su cimma yarjejeniya, da kuma batun kulla hulda da Isra'ila, wacca Saudiyyar ta ce ta riga ta bayyana matsayinta kansa kan cewa, sai Isra'ila ta lamunta da kafuwar kasar Falalsdinu wacca birnin Kudus zai zama helkwatarta kafin ta yi hulda da Isra'ilan babu kuma gudu ko ja da baya kan wannan matsayinta a yanzu koma nan gaba.
Bangaren Isra'ila
A Isra'ila dai an jiyo shugaban 'yan aawa na kasar Yair Lafid na siffanta yarjejeniyar da ake shirin cimma da Iran da wani mummunan naushi a fuskar Isra'ila da ba a taba mata irinsa ba a tarihinta.
A yanzu haka dai wata tawagar musamman ciki har da shugaban babban bankin Iran na ziyarar kasar Katar don fara shirye-shiryen kwashe makudan kudaden kasar ta Iran da ke jibge a bankunan kasar.